Dakarun kawancen na kasashen Larabawa da na kurdawaa sun farwa mayakan ISIL a yankin Raqa na Syria a yayin da kuma dakarun Iraki suka doshi yankin Fallujah domin fattakar mayakan.
Masu sa ido a rikicin na Syria sun ce mayakan na amfani da fararen hula a matsayin garkuwar yaki.
Wani dan Raqa kuma mai fafutika Abdel Aziz al Hamza wanda ya gudu zuwa Jamus yace mayakan na fakewa a gidajen fararen hula da makarantu domin tsira daga luguden wutar da ake yi masu da jiragen yaki.
Dubban mutane aka ruwaito an yiwa kawanya a yankin Raqa kuma babu yadda zasu iya ficewa daga yankin saboda yaki.